Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana damuwa bisa zargin mutuwar wasu fararen hula bayan wani hari da ta kai maboyar 'yan ta'adda a jihar Kaduna
2024-10-01 15:37:57 CMG Hausa
Sama da mutane 25 ne ake zargin sun mutu bisa kuskure yayin wani hari bom da dakarun sojin saman Najeriya suka kai maboyar 'yan ta'adda a yankin Kidandan dake yankin karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.
Mutanen da ake zargin sun mutun, sun kushi wasu masu ibada a masallaci su 23 da manoma da kuma wasu da suke gudanar da harkokin kasuwanci a wata kasuwa dake yankin, ko da yake rundunar sojin ta ce ta kai harin ne kan sansanonin 'yan ta'adda bayan ta kammala samun cikakkun bayanan sirri.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Da yake zantawa da manema labarai kansilan yankin Abdullahi Isma'il ya tabbatar da cewa hakika yankin yana da hatsarin gaske saboda yawan harkokin 'yan ta'adda.
To, amma cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar litinin 30 ga watan jiya wadda take dauke da sa hannun mataimakin darkatan yada labarai rundunar Group Kaftin Kabiru Ali ta yi bayanin cewa hakika dakarun runduanr sun kai hari ta sama a jiya litinin kuma yan ta`adda aka afkawa kai tsaye bisa aiki da kwararan bayanan sirri.
Kuma kamar yadda bayanai suka nuna 'yan ta'addan sun shafe shekaru 2 a wannan yanki, inda suke garkuwa da mutane sannan kuma suna kai hare-haren ta'addanci.
Ya ce a yayin farmakin an sami nasarar hallaka 'yan ta'adda da dama, amma dai duk da haka kamar yadda mataimakin daraktan yada labaran rundunar ya bayyana, za a bi kadin zargin da al'ummar yankin suka yi wanda ke nuna cewa an kashe mutanen da ko kadan ba su da wata alaka da ayyukan ta'addanci.(Garba Abdullahi Bagwai)