logo

HAUSA

Hadin-gwiwar Sin da Najeriya na da makoma mai haske

2024-10-01 15:02:14 CMG Hausa

Yau Talata 1 ga watan Oktoba, rana ce ta cika shekaru 75 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, kana, Najeriya ta cika shekaru 64 da samun ’yancin kai daga turawa ’yan mulkin mallaka. Al’ummomin kasashen biyu su kan shirya bukukuwa domin murnar wannan muhimmiyar rana a kowace shekara, al’amarin da ya zama wata al’ada dake shaida zumuncinsu mai karfi.

Wani muhimmin batun da ya wakana tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a bana shi ne, taron dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka wato FOCAC da aka yi kwanan nan a birnin Beijing, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping, tare da takwaransa na tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, da sauran wasu shugabannin kasashen Afirka da dama, suka hallara a kasar Sin, don tattaunawa kan yadda za su karfafa zumunci, da kara samun fahimtar juna, da habaka hadin-gwiwa don kirkiro makoma mai haske.

Bayan da suka kulla dangantakar diflomasiyya tsakaninsu shekaru 53 da suka gabata, kawo yanzu, Sin da Najeriya sun fadada hadin-gwiwa da mu’amala a bangarori daban-daban, al’amarin da ya haifar da babban alfanu ga jama’arsu baki daya. A wajen taron FOCAC na bana, shugabannin kasashen biyu sun sanar da daga matsayin huldarsu zuwa matsayin huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkanin fannoni, inda kuma suka shaida daddale wasu muhimman yarjeniyoyin hadin-gwiwa, da suka shafi tattalin arziki, da kasuwanci, da aikin noma, da sufurin jiragen sama, da watsa labarai da sauransu, al’amarin da ya bude sabon babi ga ci gaban dangantakar Sin da Najeriya.

Shirin Sin da Afirka a wannan sati, ya gayyaci masanin dangantakar Sin da Najeriya, da mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, don jin ta bakinsu game da yadda hadin-gwiwar kasashen biyu ke inganta a halin yanzu, da kuma makomar hadin-gwiwar su a nan gaba. (Murtala Zhang)