logo

HAUSA

An nuna wasannin gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni na birnin Leshan na shekarar 2024

2024-10-01 21:18:28 CMG Hausa

Jiya Litinin 30 ga watan Satumba, aka fara nuna wasannin gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni a tashar layin dogo mai saurin tafiya ta Leshan, da filin al’adu na wurin yawon shakatawa na babban ginin budda na Leshan, da kuma babban titi na Dongdajie, dukkansu  a birnin Leshan na kasar Sin, domin murnar zagayowar ranar kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin. Lamarin da ya jawo hankulan masu yawon bude ido daga wurare daban daban na kasar.