logo

HAUSA

Bangaren sadarwa na Sin ya samu tagomashi cikin watanni 8 na farkon bana

2024-10-01 15:35:18 CMG Hausa

Masana’antar sadarwa ta kasar Sin, ta yi ta samun ci gaba mai armashi cikin watanni 8 na farkon bana, inda harkokin kasuwanci masu tasowa suka ingiza ci gaba.

Daga watan Junairu zuwa na Agusta, kudin shigar da aka samu daga hidimomin sadarwa ya kai yuan triliyan 1.17, kwatankwacin dala biliyan 167.6, inda aka samu karuwar kaso 2.7 kan na bara.

A wannan lokaci, bangarori masu tasowa kamar na manyan bayanai da tsarin lissafi na Cloud da na’urori da manhajojin sadarwa, sun ci gaba da samun kuzari mai karfi.

Manyan kamfanonin sadarwa na Sin da suka hada da China Telecom da China Mobile da China Unicom, su ma kudin shigar da suka samu daga wadancan bangarori masu tasowa ya karu da kaso 10.5 a kan na bara, zuwa yuan triliyan 289.7, lamarin da ya ingiza karuwar jimilar kudin shigar bangaren da maki kaso 2.4. (Fa’iza Mustapha Jamila)