logo

HAUSA

Sojojin kasar Sin sun yi atisaye a yankin tekun kudancin kasar

2024-10-01 20:17:31 CMG Hausa

Sashen rundunar sojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin (PLA) na yankin kudancin kasar, ya shirya wani atisayen jiragen ruwan soji domin gudanar da sintirin shirin ko-ta-kwana a yankin tekun kudancin Sin

Wata sanarwa da rundunar ta kudanci ta fitar, ta ce an gudanar da sintirin ne kamar dai yadda ake tsara atisayen soji a kowacce shekara.

Ta kara da cewa, sintirin na shirin ko-ta-kwana na da nufin inganta karfin rundunar na yaki domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankalin yankin. (Fa'iza Mustapha)