logo

HAUSA

Ministan man fetur din Nijar ya kai ziyarar aiki a kasar Aljeriya

2024-09-30 10:07:09 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, ministan man fetur din kasar ya kai ziyarar aiki a ranar jiya Lahadi 29 ga watan Satumban shekarar 2024 a birnin Alger na kasar Aljeriya, a wani yunkurin farfado daga huldar dangantaka tsakanin kasashen biyu, musamman kan shirin bututun mai da zai ratsa Sahara.

Daga birnin Yamai, abokin aikin mu Mamane Ada ya hada mana wannan rahoto. 

Kokarin kawo sabon lumfashi ne ga huldar dangantaka dake tsakanin kasashen Nijar da Aljeriya, da mai da hankali kan shirin gina bututun mai da zai ratsa Sahara sun kasance muhimman batutuwa na wannan rangadi.

Ganin cewa, bangarorin biyu sun amince da ci gaba da ayyukan tabbatar da wannan gagarumin aiki, wanda ya kamata a kammala a shekarar 2027.

A yayin ziyarar aiki da ya kai a kasar Nijar, ministan makamashi na kasar Aljeriya, Mohamed Arkab, a cikin watan Augustan da ya gabata, ya shaida cewa bangaren Nijar ya dauki niyyar cika nauyin da ya rataya kan wuyansa na gina bututun mai na tsawon kilomita dubu 1, alkawarin da kuma faraministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine ya tabbatar a zuwansa Aljeriya.

Dalilin wannan ziyara tabbatar da niyyar kasashen biyu na bude sabon babi na dangantakar moriyar juna, aiwatar da ayyukan kamfanin Sonatrach a Nijar, da kuma shirin karni, cewa da bututun mai dake ratsa Sahara, in ji minista Sahabi Oumarou gaban takwaransa na makamashi na Aljeriya Mohamed Arkab.

A halin yanzu, bisa tsawon kilomita 4200 na wannan bututun mai, kilomita 1800 suka rage. Kilomita 1000 bangaren Nijar, kilomita 700 bangaren Aljeriya, kana kilomita 100 bangaren Nijeriya.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.