logo

HAUSA

A kasar Mali, mutane 75 mutu kana 148 suka ji rauni sakamakon ambaliyar ruwa

2024-09-30 10:39:26 CMG Hausa

A kasar Mali, a yayin wani taron manema labarai a ranar jiya 29 ga watan Satumban shekarar 2024, hukumar dake kula da bala’u daga indallahi ta kasa ta bayyana cewa ruwan sama na shekarar bana sun janyo ambaliyar ruwa da ta sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Mutane 75 ne suka mutu, kana 148 suka jikkata yayin da wasu mutane sama da 250,305 matsalar ambaliyar ruwan sama ta rutsa da su zuwa ranar 27 ga watan Satumban shekarar 2024, in ji shugaban hukumar kula da bala’u daga indallahi ta kasa, kanal Issa Raoul Dana Dabo.

Haka kuma kusan ambaliyar ruwa 591 aka yi rejista a kasar Mali daga ranar 1 ga watan Augustan shekarar 2024 zuwa ranar 27 ga watan Satumban shekarar 2024, a cewar wannan hukumar kula da bala’u daga indallahi, tare da jaddada cewa yankin Tombouctou ya fi cin karo da ambaliyar ruwa 196.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.