Morroco ta shirya wani zaman taro tare da kasashen yankin Sahel a birnin New York
2024-09-30 09:56:07 CMG Hausa
A dabara da babban taron MDD karo na 79, kasar Morroco ta yi amfani da wannan dama a ranar Asabar 28 ga watan Satumban shekarar 2024 domin wata ganawa tare da shugabannin diplomasiyyar kasashen yankin Sahel, a karkashin jagorancin masarautar Morroco.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Ministocin harkokin wajen kasashen Morroco, Burkina Faso, Nijar, Mali da Chadi sun yaba da wannan tattaunawa a cikin wata sanarwar hadin gwiwa, aikin da rundunar Task Forces ta kasashen biyar ya yi, wannan kuma tun zaman taron farko da ya gudana a birnin Rabat na Morroco a cikin watan Junin da ya gabata.
Ministocin sun yi nazarin shirye-shiryen da kasar Morroco ta gabatar cikin tsarin wannan shirin kasa da kasa tare da wani jadawalin ci gaban kasashen, da a yanzu haka ake ci gaba da aiwatar da su a cikin kowace kasa, in ji wannan sanarwa.
Ministocin harkokin wajen kasashen biyar sun dauki niyyar sake gudanar da wani taro domin ci gaba da ayyukan masarautar Morroco da aka kaddamar a ranar 6 ga watan Nuwamban shekarar 2023.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.