Shekaru 75 Masu Albarka
2024-09-30 19:22:35 CMG Hausa
Gobe ke bikin cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, a wadannan shekaru 75 da suka gabata, karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS), al’ummar Sinawa sun yi nasarar juyin juya halin demokradiyya, kuma sun kai matsayin da za su iya tantance makomarsu. Sai dai kuma a wannan shekarar, Dean Acheson, sakataren harkokin wajen Amurka na lokacin, a kokarin yin bayani kan musabbabin juyin juya halin kasar Sin, ta hanyar nazarin yanayin tattalin arziki da akidar kasar Sin, ya danganta juyin juya halin da abubuwa biyu wato "yawan jama'a" da "kwararar sabbin ra'ayoyi daga yamma”. Canki cankar Acheson na “yawan jama'a” ba ya da tushe. Saboda a tarihi, duk inda aka yi zalunci da cin zarafi, to dole a fuskanci turjiya, ko da yake siffofi da hanyoyin wannan turjiya na iya bambanta amma wannan ita ce mahangar tarihi.
Juyin juya halin dimokradiyya ta kasar Sin ya ruguje tsohon tsari da samar da wata sabuwar al'umma da za ta mallaki kasarta wadda za ta tsaya da kafafunta kuma da mutunci, kuma ita ce jigon ci gaban kasar. Kamar yadda gwamnatin kasar Sin ta sha nanata cewa, dan Adam ya fi komai daraja a duniya. Kuma karkashin jagorancin jam'iyyar JKS, muddin akwai mutane, za a iya samar da kowane irin abin al’ajabi.
Tun daga shekarar 1949, jam'iyyar JKS ta jagoranci al'ummar kasar wajen gaggauta farfado da tattalin arzikin kasa, wanda tsohuwar gwamnatin ta yi wa illa sosai. Duk da kasancewarta kasa mai girma da talauci mai yawan jama'a, kasar Sin ta samu ci gaba sosai wajen bin tsarin gurguzu, inda ta fara aiwatar da ayyukan gina kasar bisa tsarin gurguzu, wadanda suka shafi aikin gona na zamani, da masana'antu, da tsaron kasa, da kimiyya da fasaha.
Tun kafin kaddamar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga waje a shekarar 1978, kasar Sin ta yi nasarar kafa tsarin tattalin arzikin masana'antu da na kasa mai cin gashin kansa a hankali. Kuma ta ci gaba da zurfafa gyare-gyare a fannin tattalin arziki, yayin da take ci gaba da yin gyare-gyare a harkokin mulki, da al'adu, da al'umma, da dai sauransu bisa tsarin gurguzu. A ko da yaushe ci gaban kasar Sin ya kasance yana da alaka da duniya, kamar yadda ci gaban duniya ke bukatar kasar Sin. Kasar Sin ta yi matukar tasiri a tarihin ci gaban bil Adama. Kuma ta kasance muhimmin karfi na ciyar da dan Adam gaba. (Mohammed Yahaya)