logo

HAUSA

Yao Yanmei dake kokarin jagorantar mazauna kauyensu don farfado da karkara

2024-09-30 20:23:00 Hausa

A makon da ya wuce, mun gabatar muku labari ne game da Yao Yanmei, wata mata ta gari daga dangin noma, wadda ta yi amfani da ilmin da ta samu a jami’a, ta kuma kirkiri wani irin zane mai suna “Zane-zanen filin shinkafa ta fasahar yanka takarda”, don jagorantar manoma garinsu wajen rubuta wata almara ta farfado da karkara.

Yao Yanmei, wadda ta girma a yankunan karkara, tun tana karama, ta nuna kauna sosai ga gonaki. A yayin da take karatu a jami’a, ta soma gudanar da kasuwanci, inda ta hada kai tare da wasu abokai, don kafa wani kamfani na noman kayan amfanin gona masu tsafta. Amma, saboda ba su da kwarewa da fasahohi sosai, a cikin kasa da shekara guda, Yao Yanmei ta yi hasarar gudanar da kasuwancinta na farko.

Daga baya, Yao Yanmei ta samu aiki a wani kamfani mai kula da sha’anin noma, amma ba ta gamsu da halin da take ciki a wancan lokacin ba, don haka sai ta tsaida kudurin komawa garinsu don raya sana’a.

Bayan ta ziyarci wurare da yawa don yin bincike, ta kirkiri wani irin zane na musamman da ake yi a filin gonaki ta hanyar yanke shinkafa, wanda ke da salon zane-zanen da ake yi ta fasahar yanka takarda, Yao Yanmei ta kira irin wannan zane da suna “Zane-zanen filin shinkafa ta fasahar yanka takarda”.

Bayan ta samu goyon baya daga iyayenta, ta yi rancen kudi har RMB yuan dubu 100, don kafa kamfanin kimiyya da fasaha mai nasaba da sha’anin noma na Jinghe.

Da farko, Yao Yanmei ta yi hayar filin gonaki mai girman hekta 4 kacal, duk da cewa yankin ba ya da girma, amma ya isa ya sa ta wahala.

Ba tare da la’akari da yanayin zafi ko kuma na sanyi ba, ta ba da rahoto ga gonaki akan lokaci, wato da karfe 6 na safe kowace rana, kuma ba za ta iya komawa gida ba har sai karfe 8 na yamma. Babu bukatar amfani da na’urar yin rajista, kuma lokacin aikin gona na iya “sa ido” mai tsanani kan ko tana iya gudanar da aiki cikin lokaci ko a’a.

Amma wannan ba shi ne mafi wahala da ta sha ba, Yao Yanmei ta fada a zahiri cewa, abun da ya fi damun ta, shi ne babu mutanen dake aiki tare da ita. Ta taba gaza daukar ma’aikata saboda rashin samun isasshen ruwa da wutar lantarki, da karancin kayan aiki, da kuma muhalli maras kyau a rumfunan renon tsiro. A cewar Yao Yanmei, “Yin kirkire-kirkire kan aikin gona? Mene ne wannan? Mazauna kauyenmu ba su fahimci hakan ba, kuma ba su amince da ni ba.”

Ba ta iya yin komai, don haka ta roki mahaifiyarta da ta rika bi gida-gida don lallashin matan dake makwabtansu.

Bayan kokarin da suka yi, wasu manoman wurin sun soma amincewa da ita, har ma sun zabi aiki a kamfaninta daya bayan daya. Mazauna kauyen duk sun kware a harkar noma, Yao Yanmei ta lura kuma ta yi karatu sosai daga wajensu, hakan ya sa ta zama sabuwar manomiya wadda za ta iya sarrafa alkalami da ma farat.

Lokacin da kyawawan“zane-zanen filin shinkafa ta fasahar yanke takarda” da “mazen da aka yi da hatsi” ke shimfida a gonaki, Yao Yanmei ta yi wa kanta “umurnin soja”, wato dole ne ta biya kowane ma’aikata albashi kafin Sabuwar Shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin.

Yao Yanmei ta kara kokari don cika alkawarinta!

A waccan shekarar, kungiyoyin daukar hoto, da kungiyoyin ‘yan jarida da yawa sun zo garinsu domin yin ziyara, kuma masu bude ido da kamfanin Yao Yanmei ya karba sun kai sama da 5000. Ba wai kawai Yao Yanmei tana biyan albashi ga ma’aikatanta kan lokaci ba ne, har ma ta taimaka wa gidajen kauyen fiye da 20 su fita daga kangin talauci, inda ta kara kudin shiga ga kowane mutum da Yuan 3,000.

Yao Yanmei tana farin ciki sosai kan irin nasarar da ta cimma, ta ce, “A shekara mai zuwa, lokacin da na sake bukatar ma’aikata, da zarar na watsa labarin nan a babban lasifikar kauye, mazauna kauyen za su zo suna neman aikin yi a kamfaninmu bisa son rai.”

Yao Yanmei ta mayar da aikin gona kamar wani abu mai ban sha’awa, a sabili da haka ta soma jawo hankulan mutane kwarai da gaske. Bisa kokarin da take yi, wasu sassan gwamnatin birnin Xinzhou, ciki har da kungiyar mata, da kungiyar matasan gurguzu, da kuma kungiyar kwadago da sauran su, sun ba ta goyon baya, kuma ta zama mai tallata garinsu na Xinzhou.

Baya ga hada aikin noma na gargajiya da sana’ar yawon shakatawa na al’adu, Yao Yanmei ta kuma ci gaba da yin sabbin gwaje-gwaje. Ta fadada tushen shuka zuwa hekta 20, ta kuma kyautata ingancin kasar gona, da kuma kara amfani da filaye. Baya ga haka, bisa ga ci gaban zamani, ta gudanar da aikin sayar da kaya kai tsaye ta yanar gizo, kuma aka samu sakamako mai kyau. Har ila yau, ta kuma jagoranci ’yan uwanta na kauye don mayar da martani ga tsarin “tattalin arzikin farfajiya” da gundumarsu ta gabatar, da gina wuraren kwana a gidajen mazauna, da bude gidajen cin abinci, da dasa itatuwan ’ya’yan itace, da kuma bunkasa binciken noma, har ma da gina masana’antar gyaran amfanin gona.

Ban da haka kuma, Yao Yanmei ta jagoranci kafa wata kungiyar taimakon juna ta matasa ta raya sana’a ta gundumar Jingle. A ganin ta, “Har yanzu akwai tsofaffi da yawa a kauyen, duk da cewa sun kware a harkar gona, amma yana da wuya su karbi sabbin abubuwa.” Don haka, idan an yi fatan bunkasa ayyukan sayar da kaya ta yanar gizo, da gudanar da ayyukan kafa wuraren kwana a gidaje, da ma neman sabbin hanyoyin ci gaba, dole ne a dogara da matasa.

 

Yao Yanmei ta ce, ba shi da sauki ga matasa a yanzu su rungumi koma garuruwansu, saboda akwai wasu abubuwa masu yawa dake iya jan hankulansu a waje, kuma ko shakka babu, aikin noma ba zai kasance masana’antar samun kudi cikin sauri ba. Amma Yao Yanmei ta yi amfani da nata labarin don tabbatar da cewa, ana iya samun zabuka masu yawa a rayuwa. A cewarta, “Ina so in baiwa matasa damar ganin cewa, akwai yiwuwar gudanar da ayyuka da dama a garinmu.”

A yayin da take da shekaru 32 da haihuwa, Yao Yanmei ta yi aure, kuma a ganinta, ’yan uwa magoya bayanta ne, za ta ci gaba da kokari tare da iyalinta, za su kuma samu makoma mai kyau kan zaman rayuwarsu. Game da matakin nan gaba da za ta dauka, ta yi farin ciki da cewa, “Na yi shirin haihuwa da wuri-wuri, kuma ina sa ran ganin wannan sabon mataki na rayuwa ta.”