logo

HAUSA

“A rubuce a sama”——Labari na da Sin: An yi bikin murnar cika shekaru 75 da kafuwar sabuwar kasar Sin a New York

2024-09-30 11:18:16 CMG Hausa

 

An kaddamar da bikin murnar cika shekaru 75 da kafuwar sabuwar Sin a birnin New York na Amurka, bisa taken “A rubuce a sama”: Labari na da kasar Sin a ranar 28 ga watan nan da muka ciki.

Yayin bikin shugaban CMG Shen Haixiong ya gabarar da jawabi ta kafar bidiyo. Kazalika jakadan Sin dake kasar Amurka Xie Feng, da wakilai kimanin dari daga bangarori daban-daban dake sada zumunta da bangaren Sin da malamai da dalibai da dama sun halarci taron.

Kafofin yada labarai 1255 daga kasashe ko yankuna 70 sun ba da labarai masu nasaba da bikin, ciki har da Amurka, da Birtaniya, da Jamus, da Italiya, da Sifaniya, da Japan, da Koriya ta kudu da kungiyar kawancen kasashen Larabawa ko AL, da Indiya da Singapore da sauransu.  (Amina Xu)