logo

HAUSA

Me ya sa Sin da sauran kasashen duniya ke cin moriya tare a cikin shekaru 75 da suka gabata tun kafuwar sabuwar kasar Sin?

2024-09-30 11:07:36 CMG Hausa

 

A shekarar bana ce ake cika shekaru 75 da kafuwar sabuwar kasar Sin, wato jamhuriyar jama’ar Sin. A cikin wadannan shekaru 75 da suka gabata, Sin ta samu gagarumin ci gaba mai armashi a bangaren saurin bunkasuwar tattalin arzikinta, har ma tana more ci gabanta da duniya, inda suke samun bunkasuwa tare.

A cikin wadannan shekaru 75 da suka gabata, Sin ta rika mu’ammala, da cudanya mai kyau da kasashen duniya, don samun bunkasuwa tare, da ma gaggauta kyautata tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa da ya bi hanya mai adalci da daidaito.

Abun da aka sa gaba wajen samun moriya tare, shi ne daidaita harkokin kai yadda ya kamata, kana da raya kai tare da yin cudanya da sauran sassan duniya, A cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata, Sin ta gaggauta karkata ga hanyar samun bunkasuwar tattalin arziki ta hanyar yin kwaskwarima a dukkanin fannoni, ta yadda za a yi kokarin samun ingantacciyar bunkasuwa. Kaza lika kasar Sin ta samu bunkasuwar kai ta hanyar yin kwaskwarima, da bude kofarta ga ketare. Kana a wani bangare na daban, ta ba da gudummawarta ga wadatar da duniya bisa ci gaban da take samu, inda ta zama muhimmin jigo, da karfin ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya. Ban da wannan kuma, Sin wata kasaitacciyar kasuwa ce dake jawo karin jarin kasashen waje.

A halin yanzu, Sin tana kokarin raya sabon karfin samar da hidimomi, da hajoji masu dorewa, tana kuma kara karfin kirkire-kirkire bisa dogaro da cudanya mai zurfi tsakaninta da kasashen duniya. A sa’i daya kuma, jarin da Sin ta zubawa kasashen duniya na taka rawa wajen raya tattalin arzikin wuraren.

To ko ta yaya za a iya magance matsalar samun bunkasuwa? Kasar Sin tana kokarin fidda hanyar da ta dace, ta kuma dade tana nacewa ga tsarin tattaunawa, da gudanar da harkoki cikin hadin gwiwa, da more ci gaba tare, ta yadda ko wane mutum zai ci gajiya.

Kasar Sin ba za ta samu bunkasuwa idan ta bar sauran duniya ba, kana duniya ma tana bukatar gudunmawar Sin, wanda hakan abu ne da aka shaida tabbatuwarsa a cikin shekaru 75 da suka gabata, kuma za a ci gaba da tabbatar da shi a nan gaba. (Amina Xu)