logo

HAUSA

“A rubuce a sama”—Labarina da Sin: An yi bikin murnar cika shekaru 75 da kafuwar sabuwar Sin a kasar Canada

2024-09-30 11:14:35 CMG Hausa

 

An kaddamar da bikin murnar cika shekaru 75 da kafuwar sabuwar Sin, wato jamhuriyar jama’ar Sin a birnin Ottawa, hedkwatar kasar Canada, bisa taken “A rubuce a sama”: Labari na da kasar Sin, a daren ranar 25 ga wannan watan nan da muke ciki.

Babban rukunin gidan rediyo da talibiji na kasar Sin wato CMG, da ofishin jakadancin Sin dake kasar Canada ne suka yi hadin kai wajen gabatar da bikin. Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabarar da jawabi ta kafar bidiyo. Kuma wakilai kimanin 500 daga bangaren siyasa, da kasuwanci, da ilmi da watsa labarai na kasar Canada sun halarci bikin.

A cikin jawabinsa, Mr. Shen Haixiong ya ce, ana daukar karin cudanyar kasa da kasa, da gaggauta yin shawarwari a bangaren al’adu da sa kaimi ga mu’ammalar al’umomi daban-daban da muhimmanci, ta yadda za a fahimci ruhin al’adun Sin, da ma hadin gwiwar al’umommin kasashen daban-daban wajen kafa kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya cikin hadin kai. (Amina Xu)