logo

HAUSA

Kasar Sin ta fitar da wasu ka’idojin da aka yi wa kwaskwarima don yaba wa jaruman da suka kwanta dama

2024-09-29 21:37:31 Hausa

Kasar Sin ta fitar da wasu ka’idojin da aka yi wa kwaskwarima don yaba wa jaruman da suka kwanta dama, gabannin bikin ranar shahidai ta kasar, wadda ta fada a ranar 30 ga watan Satumba.

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya rattaba hannu kan wata doka ta majalisar gudanarwar kasar, don yada wadannan ka’idojin da aka yi wa kwaskwarima, wadda ta jaddada tabbatar da shugabancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, da kiyaye mutunci da martabar jaruman da suka kwanta dama, da kare hakkoki da muradun iyalansu.

Ka’idojin da aka yi wa kwaskwarima sun tanadi ingantattun sharudda da hanyoyin tantance shahidai, da ingantaccen tallafin kudi, da ba da fifiko ga kulawa da iyalansu, da karfafa kariya da kula da wuraren tunawa da su. Ka’idojin sun kuma bayyana bukatar karfafa yada ayyukan jarumtaka na shahidai tare da inganta ayyukan tunawa da girmama su.

Ka'idojin za su fara aiki ne a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2025. Tun daga shekarar 2014 ne kasar Sin ke bikin ranar shahidai a kowace shekara. (Yahaya)