Rawar da kasar Sin ke takawa ta fannin sauya fasalin makamashi a duniya
2024-09-29 21:52:41 CMG Hausa
Daga Lubabatu Lei
A inda a baya ake hakar kwal a birnin Datong na lardin Shanxi da ke arewacin kasar Sin, yanzu haka, an kafa jerin farantan samar da wutar lantarki ta hasken rana, wadanda tun bayan da suka fara aiki a shekarar 2016, sun samar da wutar lantarki da ta zarce KWH biliyan 12.
Lardin Shanxi da ke arewacin kasar Sin lardi ne da aka fi yawan samun kwal a kasar Sin. Sai dai yayin da ra’ayin nan na samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba ke kara zame wa al’ummar kasar jini da tsoka, a wannan yankin da Allah ya albarkace shi da kwal, ana ta samun sauye-sauye ta fannin nau’o’in makamashin da ake amfani da su. Bayan da kasar Sin ta fara gwajin yi wa fasalin makamashin gyare-gyare a lardin Shanxi a shekarar 2019, fasalin makamashi ya dinga kyautata a lardin, inda aka yi ta bunkasa samar da nau’o’in makamashi da ba za su gurbata muhalli ba, ciki har da lantarki da aka samar ta iska da rana da sauransu. Tun farkon lokacin da aka kaddamar da gwajin, wutar lantarki da aka iya samarwa ta iska da zafin rana ya zarce KW miliyan 20, amma ya zuwa karshen watan Yunin bana, adadin ya zarce KW miliyan 55.
Abin da ya faru a lardin Shanxi na daga cikin sauye-sauyen da ke faruwa a kasar Sin ta fannin tabbatar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba. Alkaluman da aka samar sun shaida cewa, fadin dazuzzukan da aka dasa a kasar Sin ya kasance na farko a duniya, kuma kasar ita ce kasar da dazuzzukanta suka fi saurin karuwa a duniya, karuwar da ta kai kimanin kaso 1/4 na duk duniya cikin shekaru kusan 20 da suka wuce. Baya ga haka, a bara, karuwar yawan wutar lantarki da ake iya samarwa ta hasken rana da karfin iska da ma sauran nau’o’in makamashi masu tsabta a kasar Sin ta ninka ta kasashen kungiyar G7 har sau hudu, ta kuma ninka ta sauran kasashen duniya gaba daya fiye da sau biyu.
Sauye-sauyen sun kuma yi daidai da ra’ayin da David Wallace-Wells ya bayyana a cikin makalar da ya wallafa a jaridar New York Times, inda ya ce, kasar Sin tana kan gaba a duniya a kokarin da ake yi na gyara yanayin da ake ciki na yawan fitar da hayaki Carbon, ya kuma misalta jerin nasarorin da kasar Sin ta cimma a wannan fanni. Ya ce, a shekarar 2023, yawan wutar lantarki da ake iya samarwa ta zafin rana ta kai GW425 a fadin duniya, sai dai adadin zai ragu har zuwa GW 162 kawai idan an cire na kasar Sin, wanda ya kai GW 263. A cikin shekaru biyar da suka wuce kuma, yawan wutar lantarki da ake iya samarwa ta zafin rana ya ninku sau takwas, a yayin da adadi na sauran sassan duniya bai kai ninki.
A makalarsa, Mr.Wallace-Wells ya nuna yabo musamman kan rawar da kasar Sin ke takawa wajen taimakawa sauran sassan duniya rage fitar da iskar Carbon. Abin hakan yake, a cikin shekaru 10 da suka wuce, kasar Sin ta zamanto ta farko a duniya a fannin samar da sabbin makamashi, hakan ya sanya, sabbin makamashi zama wani muhimmin bangaren da kasar Sin ke aiwatar da hadin gwiwa da kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka. A yankin De Aar da ke tsakiyar kasar Afirka ta Kudu, na’urorin samar da wutar lantarki ta karfin iska, suna samar da wutar lantarki sama da KWH miliyan 750 a kowace shekara, kuma ta hakan an yi tsimin kwal kimanin tan sama da dubu 200, tare da rage fitar da iskar Carbon kimanin tan dubu 700. Sai kuma a yankin Garrisa na kasar Kenya, wani kamfanin kasar Sin ya kafa tashar samar da wutar lantarki ta zafin rana irinta mafi girma a gabashin Afirka, wanda ya sassauta matsalar karancin wutar lantarki da kasar ta fuskanta, kuma ba tare da fitar da iskar Carbon ba. A kasar Nijeriya, kamfanin kera bas bas na Yutong na kasar Sin, ya samar da bas bas masu aiki da wutar lantarki a birnin Lagos, wanda shi ne karo na farko da kasar ta fara samun wannan sabon nau’in motocin bas.
Mr.Wallace-Wells ya kuma bayyana damuwarsa game da yadda kasar Amurka da ma kawayenta suke kokarin dalike bunkasuwar kasar Sin ta fannin bunkasa sabbin makamashi, bisa dalilin cewa “kasar Sin na samar da kayayyaki masu alaka fiye da kima”, kuma a ganinsa, hakan zai iya haifar da koma baya ga kasar Sin a kokarinta na samar da sabbin makamashi, wanda daga karshe zai jefa duniya cikin mawuyacin hali. Ko da yake ba sai Mr.Wallace-Wells ya damu da hakan ba, sabo da kamar yadda takardar bayani kan sauyin fasalin makamashi da kasar Sin ta fitar a karshen watan da ya gabata ta ce, sauya fasalin makamashi ya zama dole ga kasar Sin. Kasar Sin na kokarin sauya fasalin makamashi ne ba don wani ya sa mu yi hakan ba, amma sabo da mu kanmu muke fatan yin haka, kuma wannan ba aikin da muke da zabi ba ne, amma aiki ne da dole mu yi.
Tinkarar sauyin yanayin duniya da dorewar makamashi na da alaka da makomar dan Adam. Kasar Sin na son yin kokari tare da kasa da kasa, su zurfafa hadin gwiwa ta fannin sauya fasalin makamashi, don tabbatar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkanin dan Adam.