logo

HAUSA

Yankin Beidahuang ya shaida yadda kasar Sin ta samu nasarori wajen zamanantar da ayyukan gona

2024-09-29 20:30:20 Hausa

Beidahuang, wani makeken yanki ne da ba’a nome shi ba a lokacin baya, a lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin. Sakamakon matukar kokarin da aka yi, yankin Beidahuang ya zama tamkar rumbun hatsi na shekaru da dama a kasar Sin, wanda ya shaida manyan nasarorin da kasar ta samu ta fuskar zamanantar da ayyukan noma.