logo

HAUSA

Shugaban MDD ya yi matukar damuwa game da tabarbarewar al’amura a Beirut

2024-09-29 16:30:44 Hausa

Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nuna matukar damuwa kan yadda al’amura ke ci gaba da tabarbarewa a birnin Beirut na kasar Lebanon cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

Kakakin babban magatakardar MDD Stephane Dujarric ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce, babban magatakardar na MDD ya bukaci bangarori daban daban da su kara jajircewa wajen aiwatar da cikakkiyar kudurin kwamitin sulhu mai lamba 1701 na shekarar 2006 nan take, tare da tsagaita bude wuta. Ya kuma nanata yin kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza da kuma sako dukkan mutanen da ake tsare da su a wurin."

Da yammacin Juma'ar da ta gabata ne jiragen saman yakin kasar Isra'ila suka kai hare-hare ta sama kan babban ofishin kungiyar Hizbullah da ke Dahieh, lamarin da sojojin Isra'ila suka ce sun kashe Nasrallah tare da wasu kwamandojin kungiyar. Daga bisani a ranar Asabar kungiyar Hizbullah ta tabbatar da mutuwar Nasrallah.

Kazalika, kasashe da bangarorin da ke adawa da Isra'ila a yankin Gabas ta Tsakiya a ranar Asabar din sun yi kakkausar suka kan harin da Isra'ila ta kai, wanda ya yi sanadiyar mutuwar shugaban na kungiyar Hizbullah, Sayyed Hassan Nasrallah a yankin kudancin birnin Beirut na kasar Lebanon .

Kawo yanzu dai mutane 1,640 a kasar Lebanon, da suka hada da yara 104 da mata 194 ne suka mutu, yayin da wasu 8,408 suka jikkata a hare-haren da Isra'ila take kai wa kasar tun daga ranar 8 ga watan Oktoban bara, a cewar ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon a ranar Asabar. (Yahaya)