logo

HAUSA

Wang Yi: Sin na kan matsayar warware rikicin Ukraine ta hanyar sulhu

2024-09-28 16:00:18 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce har kullum kasarsa na goyon bayan adalci, da gaskiya, game da batun rikicin kasar Ukraine, tana kuma nacewa aiwatar da matakan tattaunawa, don wanzar da zaman lafiya, kana tana tsaiwa tsayin daka wajen kare zaman lafiya.

Wang ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a, yayin da yake hadin gwiwar jagorancin taron ministocin kasashen da suka amince da sabon kawancen nan mai lakabin "Kawayen zaman lafiya", wani dandali na yunkurin warware rikicin Ukraine ta hanyar lumana.

Wang, ya ce sabon dandalin kawancen ba shi da burin rungumar wani bangare na kasashen dake dauki ba dadi, ko ingiza fito na fito da wani bangare, ko maye gurbin dandaloli da ake da su, maimakon haka burin kafa shi, shi ne dogaro ga tasirin MDD wajen hado kan karin kasashe daga sassa masu saurin samun ci gaba, da masu tasowa, ta yadda za a kara yayata muryoyi na adalci, da daidaito da sanin ya kamata.

A dai jiyan, Wang Yi ya kuma halarci ganawa da ministocin wajen kasashen Sin da Rasha, da Pakistan, da Iran, game da batun kasar Afghanistan, da kuma taron manyan jami’ai na kwamitin tsaron MDD game da Gabas ta Tsakiya. Har ila yau, ya gana da babban magatakardar MDD Antonio Guterres, da ministocin wajen hadakar kasashen yankin Gulf, duka a gefen babban taron MDD dake gudana a birnin New York.    (Saminu Alhassan)