An bude babban taron ci gaban ala’du da sha’anin yawon bude ido na lardin Sichuan
2024-09-28 15:37:12 CMG Hausa
An bude babban taron ci gaban ala’du da sha’anin yawon bude ido na lardin Sichuan, kana taro karo na goma na zuba jari kan sha’anin yawon bude ido na kasa da kasa a birnin Ya’an na lardin Sichuan dake kasar Sin.
A yayin taron da aka bude a jiya Alhamis, wasu mawaka da masu jagorantar shirin talibijin, sun gabatar da wasu shahararrun wuraren yawon shakatawa da abubuwan musamman na Sichuan. Kana sun gayyaci ‘yan kasashe daban daban zuwan lardin Sichuan don yawon bude ido.