logo

HAUSA

UNICEF:kaso 69.2 na kananan yara a jihar Kano suna rayuwa cikin yanayin talauci mutuka

2024-09-28 14:59:17 CMG Hausa

Asusun lura da kananan yara na majalissar dinkin duniya ta UNICEF ya tabbatar da cewa kaso 69.2 na kananan yaran da suke rayuwa a jihar Kano ta Najeriya suna cikin yanayin na talauci sosai.

Babbar jami`a mai kula da tsare- tsaren manufofi da zamantakewa na ofsihin asusun dake jihar kano Hajiya Fatima Musa ce ta tabbatar da hakan ranar juma`a 27 ga wata a jawabin da ta gabatar yayin taron karawa juna sani da asusun na UNICEF ya shiryawa `yan jaridu da suka fito daga jahohin Kano, Katsina da Jigawa a garin Zariya ta jihar Kaduna.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Hajiya Fatima Musa ta ce kaso 69.2 na yaran da shekarunsu bai wuce daga 1 zuwa 17 ba suna cikin matsi sosai na rayuwa sakamakon talauci, yayin da kaso 59.5 kuma suke a matsakancin yanayin jin dadin rayuwa a jihar ta Kano.

Jami`ar asusun na UNICEF  ta cigaba da bayanin cewa a sakamakon binciken da asusun ya gudanar a kan mizanin talauci a tsakanin kananan yaran da suke a shiyoyin Najeriya ya nuna cewa kaso 90 na yaran da suka fito daga shiyar arewa maso gabas da kuma arewa maso yammacin kasar suna rayuwa sosai cikin kangin talauci, yayin da kuma kaso 65.1 zuwa 74 suke cikin wannan yanayi a shiyar kudu maso gabashi da kuma kudu maso yammacin Najeriya.

Jami`ar asusun na UNICEF a jihar ta Kano ta bayyana fargabar ta sosai akan yadda talauci ke kara yin katutu a tsakanin kanann yara a Najeriya, a kan haka ne ta yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai dasu kara adadin kudin da suke warewa cikin kasafin kudin ta fuskar kai dauki ga rayuwar kananan yara a bangaren kiwon lafiya, muhalli, ilimi da kuma abinci .(Garba Abdullahi Bagwai)