Har yanzu akwai kusan iyalai miliyan biyu da basa cikin muhallan su tun bayan ambaliyar ruwa a Maiduguri
2024-09-28 15:08:36 CMG Hausa
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya tabbatar da cewa, kawo yau akwai kusan iyalai miliyan 2 da basa cikin gidajen su tun bayan ambaliyan ruwan daya afku a birnin Maiduguri a farkon wannan watan na Satumba.
Gwamnan ya tabbatar da hakan ne ranar alhamis 26 ga wata lokacin da yake karbar tallafi daga wasu bankunan kasar, ya ce da yawa daga cikin wadannan iyalai suna zaune ne a sansanonin da gwamnati ta samar.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Gwamnan ya shaidawa wakilan shugabannin bankunan na Najeriya da suka bayar da gudumowar naira buliyan 1 cewa da yawa gidaje da sauran gine gine ruwa ya lalata su wanda kuma aka kiyasta cewa za a kashe dala miliyan 600 kafin a sake gyara su mutane su koma ciki da zama.
Farfesa Babagana Umaru Zulum ya tabbatarwa duniya cewa zai yi adalci wajen sarrafa kudaden da aka baiwa jihar gudunmowa, wanda tuni suke a adane a cikin wani asusu na musamman.
Ya ce hakikanin mutanen da wannan bala’i ya shafa ne kawai za su amfana da wadannan kudade ta hanyar gina masu matsuguni da samar masu da kayayyakin bukatun yau da kullum.
Rahotanni su tabbatar da cewa har yanzu dai hada-hadar kasuwanci bai kankama ba a birnin na Maiduguri tun bayan afkuwar wannan ambaliyar ruwa.(Garba Abdullahi Bagwai)