logo

HAUSA

An yi taro karon farko na kawancen cibiyoyin bincike na Sin da kasashen Larabawa

2024-09-28 20:07:56 CMG Hausa

An gudanar da taro karo na farko na kawancen cibiyoyin bincike na kasar Sin da kasashen Larabawa a birnin Shanghai a jiya Jumma’a, inda wakilan cibiyoyin bincike kusan 40 na Sin da kasashen Larabawa 19, suka tattaunawa da juna game da “inganta ci gaban Sin da kasashen Larabawa mai inganci a sabon zamani”, da “inganta tsagaita bude wuta a zirin Gaza, don warware batun Falasdinu cikin adalci a dukkan fannoni” da dai sauransu.

Wakilan kasashen Larabawa da suka halarci taron, sun yaba da kokarin Sin na warware matsaloli kamar batun Falasdinu, da kuma muhimmiyar rawa da bangaren Sin ya taka wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. (Safiyah Ma)