logo

HAUSA

Kasar Sin ta kaddamar da rigar da 'yan saman jannatinta za su sanya yayin gudanar da bincike a duniyar wata

2024-09-28 16:28:00 CMG Hausa

Hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane a sararin samaniya ta kasar Sin ko (CMSA), ta kaddamar da tsarin rigunan da 'yan saman jannatin kasar za su sanya, a lokacin da za su gudanar da ayyukan bincike a duniyar wata. A yau Asabar ne aka kaddamar da rigar, tare da neman shawarar sunan da za a baiwa rigar daga jama'a.

An nuna rigar ne a wani bikin dandalin fasahohi masu alaka da tufafin da 'yan saman jannati suke sanyawa karo na 3, wanda cibiyar gudanar da bincike, da horar da 'yan sama jannati ta kasar Sin ta gudanar, a birnin Chongqing dake kudu maso yammacin kasar Sin.

'Yan sama jannatin kasar Sin Zhai Zhigang, da Wang Yaping, sun sanya sabuwar rigar mai launin fari da jajayen ratsi, don nuna tsarinta a cikin wani bidiyon da aka watsa a wajen bikin. (Bello Wang)