logo

HAUSA

Binciken ra'ayin jama'a na CGTN: Al'ummun duniya sun nuna karin amincewa da kasar Sin

2024-09-28 19:55:00 CMG Hausa

A yayin da bikin cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin ke karatowa, gidan telabijin na CGTN, da jami'ar Renmin ta kasar Sin, sun fitar da sakamakon binciken jin ra'ayin jama'ar kasashe daban daban, wanda aka gudanar a karo na biyu, don neman jin ra'ayoyinsu dangane da kasar Sin. Inda sakamakon ya nuna cewa mutanen da suka halarci binciken, sun nuna karin amincewa da kasar Sin.

Dangane da martabar kasar Sin, kashi 92% na wadanda suka halarci binciken, suna kallon kasar Sin a matsayin wata kasa mai muhimmanci. Kana a fannin tattalin arziki, kashi 92.3% na mutanen da suka shiga binciken sun yaba da karfin tattalin arzikin kasar Sin. Yayin da a fannin kimiya da fasaha, kashi 92.3% na mutanen da suka halarci binciken sun ce karfin kasar Sin a fannin mallakar fasahohi masu inganci yana da matukar burgewa.

An dai gudanar da binciken ne kan mutane 16,400 na wasu kasashe 41. (Bello Wang)