Sin na fatan Amurka za ta kyautata mu’amalar sassan biyu bisa sanin ya kamata
2024-09-28 15:28:23 CMG Hausa
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce maimakon Amurka ta rika aiwatar da matakai na kokarin dakile Sin a hannu guda, a daya hannun kuma tana neman sassan biyu su kyautata hadin gwiwa, kamata ya yi ta mu’amalanci Sin din ta amfani da manufofi na sanin ya kamata.
Wang Yi, ya bayyana hakan ne ga sakataren wajen Amurka Antony Blinken, a jiya Juma’a a birnin New York, a gefen babban taron MDD na 79.
Wang, ya kara da cewa, ya kamata Amurka ta rungumi tattaunawa bisa martaba juna, da bunkasa hadin gwiwa na cimma moriyar juna, da magance banbance banbance bisa sanin ya kamata, maimakon yanke hukunci ta amfani da ganin dama da karfin tuwo, ko amfani da kurakuran baya, a matsayin uzurin sake aikata wasu kurakuran. (Saminu Alhassan)