logo

HAUSA

Kasar Indiya za ta inganta jirgin saman yaki samfurin Su-30MKI

2024-09-27 10:25:18 CGTN Hausa

A kwanan baya, gwamnatin Indiya ta amince da wani shirin sayen kayayyakin soja da darajarsu za ta kai dalar Amurka biliyan 3.38, domin kamfanin Hindustan Aeronautics zai sayi injin jirgin sama samfurin AL - 31FP guda 240, ta yadda zai iya inganta jiragen saman yaki samfurin Su-30MKI. (Sanusi Chen)