logo

HAUSA

An bude taron birni mai ayyukan tsara abubuwa na kasa da kasa na 2024 a Shanghai

2024-09-27 16:38:33 CMG Hausa

 

Yau Juma’a, sashen Shanghai na babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG da sauran hukumomi sun kaddamar da taron birni mai ayyukan tsara abubuwa na kasa da kasa na 2024 wato WDCC2024 a Shanghai cikin hadin gwiwa bisa jagorancin gwamnatin Shanghai da hukumar UNESCO.

Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi cewa, karfin ayyukan tsara abubuwa ya bayyana ne a fannin samun karbuwa da kirkire-kirkire da sauke nauyin dake wuya. A matsayin babban rukuni na watsa labarai a nan kasar Sin da girmansa ya kai matsayin koli a duniya dake da ayyuka mafi yawa dake kuma shafar mabanbantan bangarori mafi fadi a duniya, CMG za ta yi nazari kan hada dabarar aikin tsara abubuwa da aikin yada labarai waje guda ba tare da tsayawa ba, don kara karfin bayyana labaran Sin da kafa sabon dandalin aikin tsara abubuwa bisa fasahohi da ma kafa sabon dandalin mu’ammalar al’adu.

Shanghai ya jagoranci wannan taro a cikin shekaru 3 a jere. Taron na wannan karo mai taken “Aikin tsare abubuwa ba iyaka da sabon karfi samar da hidimomi da hajoji masu karko ”, da zummar kafa dandalin mu’amala da hadin kai ta fuskar ayyukan tsara abubuwa na kasa da kasa da nazari kan raya karfin samar da hidimomi da hajoji masu karko bisa fasahar ayyukan tsara abubuwa, ta yadda za a gaggauta raya birane da zaman rayuwa bisa wannan aiki. (Amina Xu)