CMG ya gudanar da bikin bayar da lambobin yabon musayar al’adu na Sin da Faransa a Shanghai
2024-09-27 19:47:05 CMG Hausa
A yau Juma’a ne aka gudanar da bikin bayar da lambobin yabo masu alaka da ayyukan musayar al’adu na Sin da Faransa a birnin Shanghai, bikin da babban daraktan kamfanin gungun kafofin talabijin da rediyo na kasar Sin CMG, mista Shen Haixiong ya halarta tare da gabatar da jawabi.
Cikin jawabin sa Shen Haixiong ya ce CMG a shirye yake ya ci gaba da bayar da gudummawa, ta karfafa manufofin da za su kai ga gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ta hanyar shirya irin wannan ayyuka na musayar al’adu. (Saminu Alhassan)