logo

HAUSA

Yawan cinikayyar waje ta Sin a fannin hajoji da bayar da hidimomi ya karu da kaso 4 bisa dari a Agusta

2024-09-27 20:29:00 CMG Hausa

Hukumar lura da hada hadar musayar kudaden waje ta kasar Sin, ta ce yawan cinikayyar waje ta Sin a fannin hajoji da bayar da hidimomi ya kai kudin Sin kusan yuan tiriliyan 4.18 a watan Agusta, adadin da ya karu da kaso 4 bisa dari kan makamancin lokacin bara.

Alkaluman da hukumar ta fitar a Juma’ar nan, sun kuma nuna cewa darajar hajoji da hidimomi da Sin din ke fitarwa zuwa kasashen ketare ya kai dalar Amurka biliyan 322.4, yayin da darajar su da take shigowa da su ya kai dala biliyan 263.5, adadin da ya nuna rarar dala biliyan 58.9.  (Saminu Alhassan)