logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce adadin almajirai miliyan 30 ne suke gararanba a manyan biranen kasar

2024-09-27 10:17:56 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa, a kalla adadin almajirai miliyan 30 da kuma yaran da ba sa zuwa makaranta miliyan 20 ne suke gararanba a kan titunan dake manyan biranen kasar.

Babban sakataren hukumar lura da ilimin tsangaya da na yaran da ba sa makaranta a tarayyar Najeriya Dr. Muhammad Idris ne ya tabbatar da hakan ranar Alhamis 26 ga wata a birnin Abuja yayin bikin kaddamar da kwamiti mai wakilai 8 da za su sake fasalta tsarin makarantun tsangaya da na allo a kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Dr. Muhammad Idris ya ce, gwamnati ta damu matuka da yanayin rayuwar irin wadannan yara, wanda su ma suna da hakki a wuyan gwamnati, a don haka akwai bukatar a rinka kula da su domin samar musu da rayuwa mai haske.

Dr. Muhammed Idris ya bayyana takaicin yadda wasu al’umomi ke haifar yaran da ba sa iya kula da harkokin rayuwarsu, sai dai kawai su zuba musu ido suna barace-barace a kan tituna, a kan hake ne gwamnati ke son zamanintar da tsarin karatun allo da na tsangaya domin yakar waccen dabi’a.

Kwamitin dai yana karkashin jagorancin Sheik Sayyadi Alqasim ne. (Garba Abdullahi Bagwai)