Shugaban MDD ya yi gargadi kan karuwar tashin hankali a duniya da kara yaduwa makaman nukiliya
2024-09-27 11:26:15 CMG Hausa
Yayin da duniya ke bikin ranar kawar da makaman nukiliya baki daya karo na 10, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadi a babban taron MDD karo na 79 game da karuwar tashin hankali a duniya, da sake farfadowar yaduwar makaman nukiliya.
A cikin sakonsa, Guterres ya yi tsokaci kan karuwar rarrabuwar kawuna da rashin yarda da juna, lamarin da ya kara tayar da zaune tsaye tare da tunzura sabon tseren mallakar makaman nukiliya. Ya yi kira ga kasashen duniya da su isar da sako guda cikin murya daya, wato hanya daya tilo ta kawar da barazanar nukiliya ita ce kawar da makaman nukiliya baki daya. Ya kuma jaddada hadin kai wajen kwance damara da kuma hana yaduwar makaman nukiliya. Yana mai cewa, ci gaba a fannin kawar da barazanar makaman nukiliya na karfafa ci gaba a fannin kawar da makaman nukiliya baki daya. "Dole ne kasashe su nemi ci gaba a dukkan fannonin cikin gaggawa." (Mohammed Yahaya)