Ecowas ta kebe dala miliyan 380 domin aikin sanya wuta a makarantu da asibitoci a kasashen dake yammacin Afrika
2024-09-27 10:09:33 CMG Hausa
Hukumar gudanarwar kungiyar Ecowas ta sanar da shirinta na saka jarin dala miliyan 380 wajen aikin sanya wutar lantarki a makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya a kasashe 15 dake yammacin Afrika da yankin Sahel.
Babban mashawarci a kan ayyukan samar da wutar lantarki na hukumar gudanarwar kungiyar ta Ecowas El- Hadji Sylla ne ya tabbatar da hakan ranar Alhamis 26 ga wata a birnin Abuja yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar. Ya ce Najeriya da Jamhuriyyar Benin da Chadi suna daga cikin kasashen da za su amfana.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Shi dai wannan aiki idan aka kammala shi zai fitar da al’umomi sama da miliyan 208 daga matsalar rashin wuta musamman ma dai mazauna yankunan karkara.
Mashawarcin kungiyar ta Ecowas ya ce, aikin da aka tsara gudanarwar zai samu tallafin bankin duniya da asusun samar da fasahar makamashin mai tsafta da kuma gwamnatin kasar Jamus.
Ya ce, haskaka makarantu da cibiyoyin lura da lafiya babu shakka zai kara azama da walwala a tsakanin ma’aikata da dalibai da sauran mutanen gari.
El Hadji Sylla ya tabbatar da cewa, za a fara gudanar da aikin ne a matsayin gwaji a kasashen Najeriya da Jamhuriyyar Benin, amma dai kamar yadda aka tsara aikin zai karade kasashe 15 dake kungiyar Ecowas sai kuma hudu da suke a yankin Sahel.
Jihohin Neja da Nasarawa da kuma babban birnin tarayya Abuja su ne za su fara amfana a kashin farko na aikin da za a gudanar a tsakanin watanni 18. (Garba Abdullahi Bagwai)