Zimbabwe za ta yi amfani da hadin gwiwar dandalin FOCAC wajen zamanantar da kanta
2024-09-26 12:01:28 CMG Hausa
Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, ya sanar da cewa, kasarsa za ta yi amfani da hadin gwiwar da aka kulla karkashin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika (FOCAC), wajen gaggauta zamanantar da kanta da bunkasa masana’antu da ingiza sauya tsarin tattalin arziki da zai mayar da hankali kan al’umma.
Shugaban ya sanar da haka ne jiya Laraba, yayin babban taro karo na 378 na jam’iyyar ZANU-PF mai mulkin kasar.
A cewarsa, ziyarar aiki da ya kawo kasar Sin da halartar taron dandalin FOCAC, ta samar da damarmakin zurfafa dangantaka da Sin a fannoni da dama.
Shugaban ya kara da cewa, baya ga mayar da hankali kan tattalin arziki da cinikayya, abu ne mai muhimmanci kasar ta kara hadin gwiwa da Sin a bangarori kamar na wasanni da al’adu da yawon bude ido da kafafen yada labarai. (Fa’iza Mustapha)