Sin ta daga zuwa matsayi na 11 a jerin kasashe dake kan gaba wajen kirkire-kirkire a 2024
2024-09-26 19:38:26 CMG Hausa
A yau Alhamis 26 ga wata ne hukumar dake lura da ikon mallakar fasahohi ta kasa da kasa, ta fitar da rahoton shekarar 2024, game da karfin kasashen duniya ta fuskar kirkire-kirkire.
A cikin rahoton, hukumar ta ce cikin kasashen duniya sama da 130, kasar Sin ta daga daga matsayin ta na bara zuwa matsayi na 11 a bana, kuma har yanzu ita ce daya tilo cikin kasashe masu matsakaicin kudaden shiga ta fuskar tattalin arziki, dake cikin jerin kasashe 30 na kan gaba a wannan jadawali.
Kaza lika, rahoton ya ce kasashen Switzerland, da Sweden, da Amurka, da Singapore da Birtaniya ne ke kan gaba a matsayi na daya zuwa na 5, yayin da Sin, da Turkiyya, da Indiya, da Vietnam da Philippines ke sahun gaba a jerin kasashe masu saurin bunkasar tattalin arziki ta fuskar kirkire-kirkire cikin shekaru 10 da suka gabata. (Saminu Alhassan)