Jiragen sama masu amfani da lantarki da Sin ta kera na taimakawa raya tattalin arziki
2024-09-26 07:20:58 CMG Hausa
Kwanan baya, jirgin sama samfurin RX1E-A, mai amfani da wutar lantarki dake da kujeru biyu a ciki, wanda kasar Sin ta kera da kanta, ya tashi a karo na farko a wani wurin yawon bude ido dake gundumar Yanqing na birnin Beijing, fadar milkin kasar Sin. Lamarin da ya nuna cewa, Sin ta sami gagarumin ci gaba a fannin raya tattalin arziki masu nasaba da shawagi a kusa da doron kasa.