Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin wajen G20
2024-09-26 14:42:29 CMG Hausa
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce ya kamata kasashe mambobin kungiyar G20 su sauke nauyin dake wuyansu a matsayinsu na manyan kasashe, su nuna sanin ya kamata da zama abun koyi, kuma su inganta da bunkasa tsarin tafiyar da harkokin duniya, bisa ruhin hadin gwiwa.
Wang Yi ya bayyana haka ne lokacin da ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 da ya gudana jiya, a gefen babban taron MDD.
Ministan ya kara da cewa, taron ya kaddamar da wani shirin kasa da kasa na yi wa tsarin jagorantar harkokin duniya garambawul, kuma mataki na gaba shi ne, fassara wannan shiri a aikace, da kuma mayar da burinsa zuwa sakamakon da aka cimma.
Baya ga haka, ya kuma gana da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da babban wakilin EU kan harkokin waje da tsaro, Josep Borrel da mutane daga sassa daban daban na Amurka, tare da halartar taron manyan jami’ai na hadin gwiwar kasa da kasa kan bunkasa kwarewa kan kirkirarriyar basira ta AI, wanda ya gudana a hedkwatar MDD dake birnin New York na Amurka. (Fa’iza Mustapha)