Karin Harajin Amurka Ba Zai Dakile Sashen Kere-Keren Kasar Sin Ba
2024-09-26 19:06:28 CMG Hausa
A baya bayan nan bangaren kasar Amurka na ci gaba da aiwatar da matakai daban daban na karin haraji kan hajojin kasar Sin dake shiga Amurka, musamman hajojin da suka shafi na manyan fasahohi, da ababen hawa masu hade da yanar gizo, da karafa da dangoginsu, matakin da masharhanta ke kallo a matsayin wata dabara da kokarin dakile ci gaban masana’antun kere-kere na Sin, duk da cewa hakan ba Sin din kadai zai illata ba, har ma da tattalin arzikin ita kanta Amurka.
A baya bayan nan, an ga yadda gwamnatin Amurka ta ayyana manufar kara haraji kan irin wadannan hajoji, ciki har da karin harajin kaso 100 kan ababen hawa masu aiki da lantarki ko EVs kirar kasar Sin, da karin kaso 50 bisa dari kan sassan na’urar samar da lantarki ta amfani da hasken rana ko solar, da karin kaso 25 bisa dari kan karafa da goran ruwa, da batiran EVs, da sauran wasu sanadarai masu nasaba, manufar da a cewar ofishin wakilcin cinikayya na Amurka za ta fara aiki tun daga ranar Juma’a 27 ga watan nan.
Har kullum ’yan siyasar Amurka na amfani da batun karin haraji, da sauran karin matakan baiwa kasuwar gida kariya, a matsayin makamin dakile kasar Sin ta fuskar takarar cinikayya. To sai dai kuma irin wadannan matakai sun ci karo da kyakkyawan tunani na cimma nasarar raya cinikayya, da bunkasa tattalin arziki tsakanin kasashen duniya.
Tuni kasar Sin ta samar da tsari mai juriya na raya fannin kere-kere, wanda ke dogaro ga tarin basirar dake cikin kasar, da babbar kasuwar ta mai yalwa, don haka ba ta dogaro ga neman alfarmar wata kasa dake ketare wajen cimma burinta na raya kai.
Hakan na iya kara bayyana a fili, idan muka kalli kwarya-kwaryar rahoton da hukumar lura da ikon mallakar fasaha ta kasa da kasa ta fitar game da alkaluman kere-kere na duniya ko (GII) na shekarar 2024, wadanda suka nuna cewa, Sin na da tarin cibiyoyin kere-keren kimiyya da fasaha har 26, cikin jimillar 100 dake kan gaba a duniya, ta kuma tabbatar da matsayinta na jagora a duniya a wannan fanni a tsawon shekaru 2 a jere.
Ko shakka babu matakan baiwa kasuwa kariya ba za su warware ginshikan matsalo da kasar Amurka ke fuskanta ba, musamman a fannin takara tsakanin masana’antu. Kuma ta hanyar dora laifi ga kasar Sin, Amurka na kaucewa sahihan matakai da ya kamata ta dauka na bunkasa tattalin arzikinta. Don haka lokaci ya yi da Amurka za ta yi karatun ta nutsu, ta yi hangen nesa, tare da karkata akala zuwa ga sauye-sauye a cikin gida, da zakulo hanyoyin raya kai, maimakon baiwa kasuwa kariya, ko yin fito na fito da kasar Sin. (Saminu Alhassan)