Sin ta kira taron nazarin yanayi da aikin raya tattalin arzikin kasar
2024-09-26 14:32:30 CMG Hausa
Ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS), ya kira wani taro a yau Alhamis karkashin jagorancin babban daraktan kwamitin kolin jam’iyyar Xi Jinping, don nazarin halin da ake ciki a bangaren raya tattalin arziki, tare da shimfida ayyukan da za a gudanar nan gaba. Taron na ganin cewa, tun farkon wannan shekara da muke ciki, tattalin arzikin Sin na tafiya yadda ya kamata, inda aka samu ci gaba ba tare da tangarda ba, kuma al’ummar kasar na cikin kwanciyar hankali. Taron ya yi nuni da cewa, fifikon tattalin arzikin Sin bai sauya ba, wato ingantaccen tushe da kasuwanni masu girma, yana kuma da sirrin samun bunkasuwa da sauransu. Ko da yake, ana fuskantar wasu sabbin matsaloli, dole ne a yi hangen nesa a duk fannoni kan halin da ake ciki, da magance kalubale da kuma karawa kai kwarin gwiwa, kana da tabbatar da sauke nauyin gudanar da harkokin raya tattalin arziki. Ban da wannan kuma, an ce, ya kamata a mai da hankali kan wasu muhimman abubuwa da daukar matakan da suke dacewa da tabbatar da manufofin da aka tsayar da gaggauta gabatar da sabbin manufofi bisa halin da ake ciki, har ma da kokarin tabbatar da muradun bunkasuwar tattalin arziki da al’umma a wannan shekara da muke ciki, bisa wadannan nagartattun manufofi. (Amina Xu)