Adadin tashoshin sadarwa na 5G ya kai miliyan 4 a kasar Sin
2024-09-26 11:56:02 CMG Hausa
Alkaluma daga ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, sun nuna cewa zuwa karshen watan Agusta, adadin tashoshin samar da sadarwar 5G a kasar ya zarce miliyan 4.04.
Adadin na wakiltar kaso 32.1 na jimilar tashoshin samar da tsarin sadarwar wayar salula dake kasar, a yayin da adadin al’ummar kasar masu amfani da sadarwar 5G ya kai miliyan 966.
Tsarin sadarwar na 5G da ma yadda ake amfani da shi, ya samu ci gaba cikin sauri a shekarun baya-bayan nan. Kuma yanzu haka, ya game birane da garuruwan kasar Sin, har ma da sama da kaso 90 na yankunan karkara.
Ma’aikatar ta kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da inganta raya tsarin na 5G da fadada shi zuwa karin wurare kamar na yawon shakatawa da raya al’adu da wuraren kiwon lafiya da jami’o’i da tashoshin sufuri da na jiragen karkashin kasa. (Fa’iza Mustapha)