Wang Yi: wasu kasashe 'yan tsiraru ciki har da Amurka ba za su samu goyon baya kan siyasantar da hakkin Bil Adam ba
2024-09-26 11:05:56 CMG Hausa
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da babban jami’i mai kula da harkokin kare hakin Bil Adam na MDD da takwarorinsa na kasashe daban-daban a ran 24 ga wata, inda ya bayyana cewa, yayin taron kwamiti mai kula da harkokin kare hakkin Bil Adam na MDD da ake gudanarwa a Geneva, wasu kasashe 'yan tsiraru ciki har da Amurka sun shafawa kasar Sin bakin fenti bisa hujjar batun Xinjiang. Ya ce da ganin hakan, kasashe kimanin 80, ciki har da kasashen musulmi da yawa, sun nuna goyon bayasu ga kasar Sin ta hanyar gabatar da jawabi cikin hadin gwiwa, kuma sauran wasu kasashe fiye da 20 sun bayyana rashin jin dadinsu kan lamarin, tare da goyon bayan matsayin da Sin take dauka, suna masu adawa da siyasantar da batun hakkin Bil Adam da adawa da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar ta hanyar amfani da wannan batu.
A cewar Wang Yi, matsayin da wadannan kasashe fiye da dari suka dauka na nuna cewa, siyasantar da batun hakkin Bil Adam da wasu kasashe 'yan tsiraru ciki har da Amurka suka yi, ba zai samu amincewa daga al’umommin duniya ba.
Ministan ya ce, matakin da wasu kasashe 'yan tsiraru ciki har da Amurka ke dauka, na bayyana yadda suke nuna fuska biyu. Ya kuma ce, a bana ake cika shekaru 75 da kafuwar sabuwar kasar Sin, kuma ci gaban da Sin take samu na kare hakkin Bil Adam na samun karbuwa a duniya, daga cikinsu akwai bunkasuwar yankin Xinjiang na a zo a gani. Ya ce kofar Sin a bude take ga duniya, ana maraba da abokai su ganewa idonsu ainihin halin da Sin take ciki. Gani ya kori ji, kuma karya fure take bata ’ya’ya, don haka, ba za a cimma nasarar shafawa kasar Sin bakin fenti ba ko kadan.
Ban da wannan kuma, yayin da Wang Yi ya halarci babban taron tattaunawa kan batun Ukraine da kwamitin sulhu na MDD ya gudanar a New York, hedkwatar majalisar, ya gabatar da shawarwari guda 3, wato na farko dole ne a dauki batun shawo kan halin da ake ciki da muhimmanci, na biyu, a karfafa gwiwar bangarori daban-daban da su yi shawarwari don magance matsalar cikin lumana, na uku kuma, ya kamata a kara karfin magance mummunan tasirin da matsalar ke haifarwa ga sauran kasashe. (Amina Xu)