logo

HAUSA

Sin na adawa da matakin cin zarafi na Amurka a tekun kudancin kasar

2024-09-26 20:34:32 CMG Hausa

Da yammacin yau Alhamis, ma’aikatar tsaron kasar Sin ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda kakakin ta, kuma babban janar Zhang Xiaogang ya amsa tambayoyin manema larabai.

Dangane da abubuwa da suka shafi tekun kudancin kasar Sin, dake cikin sanarwar da aka fitar a gun taron kolin "Tattaunawa kan tsaro na bangarori hudu", wato tsakanin shugabannin Amurka, Japan, Indiya, da Austriliya, Zhang Xiaogang ya ce, Sin na adawa da ayyukan dake iya tayar da rikici, ko ta’azzara yanayin tashin hankali a tekun kudancin Sin.

Ya kuma kara da cewa, Amurkan ta yayata cewa, wai "Barazanar soja ta kasar Sin" a ko da yaushe. Kaza lika, ya zuwa watan Satumban shekarar bana, jiragen sama masu leken asiri na Amurka sun yi shawagi har kimanin 1500 cikin yankunan Sin, don bincike da kuma haifar da barazana. Wanda hakan ke nuni da cewa, bangaren Amurka ya zama tabbataccen mai tsokana, mai tayar da hankali, kana mai kawo cikas. (Safiyah Ma)