logo

HAUSA

Sin na fatan inganta karfin sassan kasa da kasa don cin moriyar fasahohin AI

2024-09-26 20:16:07 CMG Hausa

 

A yau Alhamis ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda a yayin taron wani dan jarida ya tambaye shi game da taron manyan jami’ai wanda Sin da sauran kasashen da abun ya shafa suka gudanar tare, kan hadin gwiwar kasa da kasa a fannin gina karfin fasahohin kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI, a yayin tattaunawar babban taron MDD karo na 79.

Game da hakan, Lin Jian ya ce an gudanar da taron bisa jagorancin Sin da Zambia, a hedkwatar MDD dake birnin New York a jiya Laraba. Kuma a gun taron, shirin amfanar da jama’a ta hanyar gina karfin fasahohin AI, ya samu goyon baya, da karbuwa daga bangarori daban daban. Kaza lika, kasar Sin na fatan inganta karfin kasashen duniya wajen cimma moriyar fasahohin AI tare, don samun makoma mai kyau ta fasahohin AI.

Game da rikicin Ukraine, Lin Jian ya bayyana cewa, Sin ta dade tana kan matsayin adalci game da wannan batu, kuma ta himmantu wajen ganin an saukaka yanayin tashin hankali da ake ciki. (Safiyah Ma)