Bitar wasannin Firimiyar kasar Ingila
2024-09-26 15:30:59 CRI
Wasannin kwallo na firimiyar kasar Ingila da aka buga cikin makon jiya sun kayatar, sun kuma nuna inda aka sa gaba, game da makomar kungiyoyin dake buga gasar ta firimiya, inda tuni wasu masu horas da kungiyoyin suka fara dariya, yayin da wasu ke fuskantar matsin lamba.
Cikin wasannin da suka ja hankali akwai na Manchester City, mai rike da kambin gasar a kakar da ta gabata, wadda ta taka leda da Arsenal ta kuma kare kan ta daga shan kunya, domin kuwa sun tashi wasan karshen mako ne da ci 2 da 2 a gidan City din. Masu fashin baki a fannin wasanni na ganin City ta yi rawar gani, duba da cewa a karshen kakar bara ma Arsenal ce ta biyu, kuma a yanzu ma ita ce ta biyu a kan teburin firimiyar.
Kafin nan City ta buga kunnan doki maras ci tare da Inter Milan a ranar Larabar makon jiya, kwana guda kafin ta fafata da Arsenal, yayin da kuma Arsenal din ta tashi na ta wasan kunnen doko ba ci tare da Atalanta a ranar Alhamis.
Duk da cewa kocin Man City Pep Guardiola bai yi manyan sauye sauye a wasan kungiyarsa na ranar Laraba ba, ya sanya ‘yan wasa Phil Foden, da John Stones, da Kyle Walker, da Ilkay Gundogan a tawagar farko ta kungiyar.
A wasan gaba ana ganin Arsenal ba za ta fafata tare da ‘yan wasan ta Martin Odegaard, da Mikel Merino ba, ko da yake Declan Rice zai dawo bayan rasa damar buga wasan makon jiya, ko da yake dai Arsenal din ta yi nasarar wasanta da ya gabata da Tottenham.
A daya bangaren kuma, West Ham da Chelsea sun bude wasan ranar Asabar din makon jiya bisa nuna kwarewa. Kaza lika, wasan Manchester City da Aston Villa masana na ganin za a kai ruwa rana, haka ma wanda za a buga da Chelsea a filin wasa na birnin London.
Nasarar da Chelsea ta samu ta lashe wasan ta ya baiwa kocin ta Enzo Maresca kwarin gwiwa, bayan fuskantar yanayin zafi mai wahalar gaske tun bayan kama aikin sa na horas da kungiyar.
Liverpool ta yi rashin nasara a gida hannun Nottingham Forest, kafin ta yi nasara da ci 3 da 1 a wasan da ta fafata da AC Milan, wanda hakan ya mayar da Liverpool din sahun gaba gabanin karawa da Bournemouth.
A nata bangare Bournemouth karkashin jagorancin kocin ta Andoni Iraola sun gamu da rashin nasara yayin wasan ta da Chelsea, don haka wasan ta da Liverpool zai nuna inda kungiyar ta dosa.
A nata bangare kuwa, Manchester United ta doke Southampton da ci 3 da nema, bayan nan kuma ta lallasa Barnsley da ci 7 da nema a wasan “League Cup”. Yanzu haka dai aikin dake gaban kocin kungiyar Erik ten Hag a fili yake, wato tunkarar wasa da Crystal Palace cikin kwarin gwiwa da nufin cimma nasara.
A kakar wasan da ta gabata, Palace karkashin jagorancin kocin ta Oliver Glasner, ta lallasa Manchester United da ci 4 da nema. Don haka a kakar bana ma ana ganin za ta taka rawar gani, duk da cewa har yanzu ba ta cimma wata babbar nasara ba, inda a wasannin ta 4 da suka gabata, ta yi kunnen doki 2 ne kadai, don haka wasu ke ganin Manchester United na iya samun nasara a kan Palace din.
Aston Villa ma ta yi nasara a wasan ta da Young Boys, karkashin jagorancin Unai Emery. Kana nasarar ta kan Wolverhampton Wanderers ta baiwa Aston Villa damar dagawa saman teburi cikin jerin kungiyoyi 4 na farko, kasancewar abokiyar fafatawar ta na can kasan teburi da maki daya.
A daya bangaren kocin Wolves Gary O'Neil, na cikin yanayi na matsi, kuma duk da cewa zai iya kuka da yanayin sauyin shekarar ‘yan wasa, wanda ya sanya kungiyar ta yi rauni, duk da haka yana bukatar cin wasa na gaba domin fita daga yanayin koma baya da kungiyar ke fuskanta.
Shi ma kocin Everton Sean Dyche, na kan gaba cikin masu horas da ‘yan wasa dake shan matsi sama da saura, duba da cewa Everton din ta fara wasannin ta da kafar hagu a kakar bana, inda Southampton ta fitar da ita daga gasar cin kofin “League Cup” cikin tsakiyar makon na jiya. Masu sharhi na ganin idan Leicester ta doke Everton, hakan na iya raba Dyche da aikin sa na horas da kungiyar, duk da cewa matsalolin Everton sun haura batun mutum guda.
Har ila yau, cikin kungiyoyin dake fama da matsaloli a firimiyar Ingila akwai Tottenham, wadda ke da maki 4 cikin wasanni 4 da ta buga, baya ga wasan da ta kwashi rashin nasara a gida, da wasan da ta sha wuya a gida tare da Brentford, wanda hakan ya sa masoya kungiyar ke ganin anya kuwa kocin ta Ange Postecoglou zai iya fitar da su kunya.
A nata bangare Brentford ta yi rashin nasarar lashe maki, yayin wasan ta da Manchester City a makon jiya. Amma duk da hakan, karkashin jagorancin kocin kungiyar Thomas Frank, suna taka wasa mai kayatarwa, wanda ake ganin na iya baiwa Tottenham Hotspur matsala, duk da cewa Brentford din za ta buga wasa na gaba ba tare da dan wasan ta Yoane Wissa ba, wanda ke fama da rauni a idon sawunsa.
Kungiyoyin Brighton da Nottingham Forest sun tashi wasan karshen mako kunnen doki 2 da 2, kuma ana ganin dukkanin su suna cikin yanayi mai kyau duk da gazawarsu ta lashe manyan gasanni a shekarun baya bayan nan.