logo

HAUSA

Ina dalilin da ya sa Amurka ke shirin daina amfani da manhaja da injuna kirar Sin a motoci masu kama Intanet?

2024-09-25 13:31:06 CMG Hausa

 

Ma’aikatar kula da kasuwanci ta kasar Amurka ta ba da shawarar daina amfani da manhaja da injuna kirar Sin a motoci masu kama intanet da maras matuki a ran 23 ga watan nan, lamarin ya kawo shakku da zargi matuka tsakanin al’umommin duniya.

A cikin shekara daya da ta gabata, Amurka ta rika daukar jerin matakai kan sha’anin samar da motoci na Sin. Kafofin yada labarai na ketare, ciki har da Reuters na ganin cewa, dalilin da ya sa Amurka ta yi haka shi ne, hana motocin dake da ingantaccen karfin yin takara da Sin ta kera shiga kasuwar Amurka, ta yadda za ta iya samun isashen lokacin kafa tsarin samar da irin wadannan motoci.

Ban da wannan kuma, CNN ta lura da cewa, takara ta kara zafi tsakanin jam’iyyu biyu na kasar duba da cewa babban zaben kasar na karatowa, kuma daukar matakai masu tsanani kan kasar Sin dabara ce dake iya jan hankali masu kada kuri’u.

Haka kuma, jaridar The New York Times ta wallafa wani sharhin inda ta yi rangadin cewa, kada gwamnatin Amurka ta kebe kasuwar motocinta daga sauran sassan duniya, domin zai sa wannan sana’a ta yi fama da koma baya, tare da sanya amfani da manyan motoci masu tsada dake shan man fetur sosai. (Amina Xu)