Daruruwan kasashe sun sake nuna matsayinsu na goyon bayan kasar Sin a MDD
2024-09-25 20:00:31 CMG Hausa
A yau Laraba, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda ya yi tsokaci game da yadda kasashe da dama suka nuna ra'ayinsu game da matsayin kasar Sin kan batutuwan da suka shafi jihar Xinjiang, da Hong Kong, da Xizang wato Tibet, a gun taro karo na 57, na kwamitin kare hakkin bil'adama na MDD.
Lin Jian ya ce, kasashe da dama sun sake bayyana matsayinsu na goyon bayan kasar Sin a MDD, wanda ya shaida cewa, yunkurin Amurka da wasu kasashen yammacin Turai na siyasantar da al'amurran da suka shafi hakkin bil'adama, ba zai samu goyon baya tsakanin al'ummun duniya ba, kuma ba zai yi nasara ba.
Game da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha karkashin yanayin dunkulewar duniya baki daya, Lin Jian ya ce, kasar Sin ba ma kawai ta kasance mai shiga tsakani ba ce, ko mai cin gajiyar tsarin dunkulewar duniya baki daya, har ma ta kasance mai ba da gudummawa, kuma mai sa kaimi ga bunkasuwar tsarin.
Kaza lika kasar Sin za ta ci gaba da inganta hadin gwiwar kasa da kasa, da ci gaba da ba da gudummawar hikimarta, don gina kyakkyawan gida guda ga dukkanin bil Adama. (Safiyah Ma)