An kama wasu mutane daga cikin na kusa da shugaban kasa Patrice Talon a birnin Cotonou
2024-09-25 13:47:11 CMG Hausa
A Benin inda a ranar jiya Talata 24 ga watan Satumban shekarar 2024, jami’an tsaro su ka yi wasu kame kame na wasu shika shiken mutane guda uku na hannun daman shugaban kasar Benin Patrice Talon.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
A halin yanzu dai gwamnatin kasar Benin ba ta ba da wani karin haske ba, ko kuma wasu labarai da suke nasaba da wadannan kame-kame, amma kuma rahotanni na kasar sun rawaito cewa wasu manyan kusoshi uku suka shiga hannun jami’an tsaro, daga akwai Olivier Boko, wanda a cewar jaridar Olofofo, wajen karfe 2 na ranar Talata 24 ga watan Satumban shekarar 2024 na dare aka kama wannan abokin shugaba kasa Patrice Talon da ke ma lakabin sunan mataimakin shugaban kasa.
A cewar wannan majiya, mutanen da ba’a tantance su ba suka zo suka yi awon gaba da wannan dan siyasa.
Sai kuma, Oswald Omeky, tsohon ministan matasa da wasannin motsa jiki, shi ma na kusa da shugaba Patrice Talon da jami’an tsaro na garde Republicaine suka kama shi da safe, da kuma har yanzu ba’a da labarinsa.
Homeky, ya yi marabus daga cikin gwamnatin kasar yau da kusan shekara guda tare da kasancewa shugaban shirin kamfen zaben shugaban kasa game da takarar Olivier Boko.
Sai kuma na uku, kanal Djimon Dieudonne Tevoedjre, kwamandan jami’an Garde Republicaine, a cewar jaridar Olofofo.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.