logo

HAUSA

Hukumomin MDD sun bayyana damuwa game da ta’azzarar rikici tsakanin Isra’ila da Hezbollah

2024-09-25 14:18:22 CMG Hausa

Hukumomin MDD sun bayyana damuwa game da karuwar rikici tsakanin Isra'ila da kungiyar Hezbollah.

Ravina Shamdasani, kakakin kwamishinan kula da hakkin dan Adam na MDD Volker Turk, ta bayyana yayin wani taron manema labarai a jiya cewa, lamarin wanda ya kai ga mutuwa da jikkata mai tsanani ga fararen hula ciki har da yara da jami'an lafiya, ka iya zama batu na keta dokar kasa da kasa, kuma ya cancanci a aiwatar da cikakken bincike mai zaman kansa, kuma bisa gaskiya.

Ta kuma bayyana cewa, kwamishinan na kira ga dukkan kasashe da masu fada a ji, a ciki da wajen yankin, da su dauki matakin kare ta'azzarar yanayin tare da tabbatar da an girmama dokokin kasa da kasa yadda ya kamata.

A cewar ministan lafiya na Lebanon Firas Abiad, daga ranar Litinin zuwa yanzu, adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar munanan hare-haren Isra’ila kan kudanci da gabashin Lebanon, ya kai 558, ciki har da yara 50 da mata 94, kana adadin wadanda suka jikkata ya kai 1835. (Fa'iza Mustapha)