logo

HAUSA

Ya zama wajibi a ci gaba da karfafa tushen aikin gona

2024-09-25 07:44:14 CGTN Hausa

Bayanai na baya-bayan nan da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, yawan amfanin hatsi na kasar Sin ya karu akai-akai tun daga shekarar 2012. Yayin da a shekarar 2015, yawan hatsin ya haura tan miliyan 650, wata muhimmiyar nasara ce da kasar ta ci gaba da kiyayewa tsawon shekaru tara a jere. Ya zuwa shekarar 2023, yawan hatsin da kasar Sin ta samu kan kowane mutum ya kai kilogiram 493, adadin da ya zarce matsakaicin adadi na duniya tsawon shekaru a jere. Duk da illolin da bala'u min indillahi da sauran kalubale suka haifar a bana, kasar Sin ta samu karuwar amfanin gona na noman rani, da tabbatar da samar da shinkafa mai girma da wuri, kana tana sa ran za a sake samun girbin hatsi mai yawa, wanda zai ba da goyon baya mai karfi don karfafawa da kara farfadowar tattalin arzikinta da samun ci gaba mai inganci. Wanda ya kara karfafawa manoma gwiwa a bikinsu na giribi karo na bakwai da ya gudana a ranar 22 ga Satumba. 

Tsarin noman hatsi na kasar Sin ya canja daga dabarun samun hatsi da yawa kadai zuwa ga dabarun daidaita yawan hatsi da aka noma da kuma ingancinsu. A shekarar 2023, kasar ta bunkasa sama da hekta miliyan 66.7 na filayen noma masu inganci. Gabadaya adadin injina na shuka da girbin amfanin gona a fadin kasar yanzu ya zarce kashi 73 cikin dari.  

Don ci gaba da zamanantar da kasar Sin, ya zama wajibi a ci gaba da karfafa tushen aikin gona na kasar, tare da sa kaimi ga farfado da yankunan karkara gaba daya. Shugaba Xi Jinping ya ce, dole ne a yi duk mai yiwuwa wajen habaka fa'idar tattalin arzikin aikin gona, da kara yawan kudin shiga ga manoma, da samar da karin kuzari a cikin karkara, da samar da fa'ida ta gaske ga manoma, ya kuma jaddada wajibcin bunkasa masana'antu na musamman yadda ya kamata. Ya ambaci wasu nasarorin da aka samu, ciki har da sana'ar bakar naman lemar kwado. Kana ingantattun masana'antu na musamman na cikin gida da sabbin masana'antu da sabbin fasahohin kasuwanci a yankunan karkara sun kara karfafa farfado da yankunan karkara na kasar Sin. A rabin farkon bana, yawan kudin shigar kowane mutum dake zaune a karkara ya kai yuan 11,272 kwatankwacin dalar Amurka 1,598, wanda ya karu da kashi 6.6 bisa 100 a zahiri. Karuwar da ya kai kashi 2.1 sama da na mazauna birane. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Mohammed Yahaya)