An fitar da matakai 24 na ingiza samar da guraben ayyukan yi masu inganci a Sin
2024-09-25 21:16:00 CMG Hausa
A yau Laraba ne kwamitin kolin JKS, da majalissar gudanarwa ta kasar Sin, suka fitar da "Ra’ayoyi game da aiwatar da dabarun samar da guraben ayyukan yi mafiya muhimmanci, da guraben ayyuka masu matukar inganci da dorewa”. Ra’ayoyin na kunshe da dabaru 24 na ingiza nasarar hakan.
Cikin dabarun, akwai fadada hanyoyin samar da ayyukan yi ga daliban da suka kammala karatu a kwaleji, da sauran matasa, da fadada guraben ayyukan yi a yankunan karkara, da bunkasa kudaden shigar su, da ingiza karuwar kudaden albashin ‘yan kwadago, da fadada matakan tallafawa rayuwar al’ummun kasa da sauran su. (Saminu Alhassan)