logo

HAUSA

Ministocin kasashen yankin Sahel AES sun sanar da wani shirin tauraron dan adam na sadarwa da na gano nesa

2024-09-25 08:54:59 CMG Hausa

 

Ministan sadarwa na Nijar, Sidi Mohamed Raliou, da ministan kudin Burkina Faso, dokta Aboubacar Nacanabo, sun kammala zaman taro a birnin Bamako tare da takwarorinsu na Mali Alhamdou Ag Ilyene, ministan sadarwa da kuma Alhousseini Sanou, ministan kudi, ranar jiya Talata 24 ga watan Satumban shekarar 2024.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada, ya aiko mana da wannan rahoto.

Wadannan ministoci sun yi aiki cikin hadin gwiwa yadda ya kamata domin samarwa kasashen yankin Sahel na AES da tauraron dan adam na sardarwa da na gano nesa.

Ministocin AES sun tabbatar da wannan shirin hadin gwiwa tare da wani kamfanin kasar Rasha, da ya shafi wannan muhimmin aiki na makomar wadannan kasashe.

A cewar minista Sanou, wannan tauraron dan adam da ya shafi harkokin sadarwa zai baiwa kasashen AES wata dama na watsa shirye shiryensu na talabijin da na rediyo cikin shiyyar.

Haka kuma, da samar da intanet mai karfi da na wayar salula a cikin yankunan da ke wuyar kaiwa da kuma suke fama da karancin gine-ginen sadarwa.

Wadannan tauraron dan adam biyu za su taka muhimmiyar rawa wajen karfafa cin gashin kan kasashen AES game da ci gaban fasahohin zamani.

A nasa bangare, minista Sidi Mohamed Raliou ya bayyana cewa, tauraron dan adam na sadarwa zai kyautata gine-ginen ababen more rayuwa a fannin sadarwa cikin shiyyar da kai ga ayyukan yanar gizo cikin sauki.

A yayin da tauraron dan adam na gano nesa zai taimaka wajen kula da albarkatu, sanya ido kan muhalli, da kuma kula da fannin tsaro, ta yadda za’a rigakafin tashe-tashen hankali a yankin Sahel.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.